Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An rantsar da Karzai a matsayin shugaban Afghanistan - 2004-12-07


Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai ya karbi ragamar mulki tare da jan hankali kan hatsarin da ke tattare da ta'addanci da kuma safarar miyagun kwayoyi. Mista Karzai ya yi rantsuwar fara aiki ranar talata abinda ya sanya ya zama zababben shugaban kasar Afghanistan na farko. Manyan baki daga kasashen waje wanda suka hada da mataimakin shugaban kasar Amurka , Dick Cheney da babban wakilin majalisar dinkin duniya, Lakhdar Brahimi sun halarci bikin mai cike da tarihi.

A jawabinsa , shugaba Karzai ya lura cewa har yanzu ta'addanci babbar barazana ne ga Afghanistan. Har yanzu burbushin 'yan Taliban da aka kawar daga mulki a shekara ta dubu biyu da daya na kai hare-hare kan sabuwar gwamnatin. Mista Karzai ya sha alwashin yaki da noman opium abar da aka tabbatar da cewa tana samar da kudin shiga ga 'yan tawayen kasar da kuma yakar cin hanci da rashawa a harkar mulki.

XS
SM
MD
LG