Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe wani babban jami’in gwamnatin Iraqi - 2004-12-16


‘Yan sandan Iraqi sun ce wasu ‘yan bindiga wadanda ba a san ko su wanene ba sun harbe wani babban jami’in ma’aikatar sadarwar kasar. ‘Yan sandan suka ce an kashe Qassim Mehawi ne bayan da aka harbe shi da bindiga daga cikin wata mota a lokacin da ya ke tafiya zuwa wurin aikinsa ranar Alhamis. Manyan jami’an gwamnatin Iraqi sun kasance wadanda ‘yan tawaye ke kai wa hari akai-akai saboda 'yan tawayen na zarginsu da hada kai da sojojin kawancen da Amurka ke jagoranta .

A wata sabuwa kuma a jiya ne a aka fara kamfen din babban zaben kasar Iraqi wanda ake sa ran za a yi ranar talatin ga watan Janairun sabuwar shekara. Daruruwan mutane na takara a dai-daiku ko cikin kawance. Firaministan rikon kwarya, Iyad Alawi na jagorantar kawancen ‘yan takara dari biyu da arba’in . Haka kuma wani babban dan siyasa a bangaren mabiya Sunni, Adnan Pachachi wanda da ya nemi da a kauracewa zaben yanzu yana yin takarar. Majalisar dinkin duniya ta ce tana shirin bude ofisoshi a Basra da Erbil domin jaddada kasancewarta a cikin kasar kafin zaben.

XS
SM
MD
LG