Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana iya hana kamuwa da sankarar bakin mahaifa - 2004-12-20


Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce kusan mata dubu dari biyu da hamsin yawanci a kasashe masu tasowa ke mutuwa a duk shekara sakamakon cutar sankarar bakin mahaifa. Hukumar ta ce za a iya kare wannan mace-mace ta hanyar gano cutar da wur-wuri. Hukumar lafiyan ta ce cutar sankarar bakin mahaifa ta fi jawo mace-macen mata fiye da a lokacin nakuda a duk shekara.

Ta kuma bayar da kididdigar cewa ana samun sababbin masu kamuwa da cutar guda dubu dari biyar a duk shekara kuma rabin matan sukan mutu sakamkon wannan cutar kuma wannan mace-mace sun fi yawa ne a yankin Afirka kudu da Sahara da kuma yankin Asiya da Latin Amurka. Darektan kungiyar kwararru masu bincike kan cutar sankara na hukumar lafiya ta duniya , Peter Boyle ya ce nan da shekara ta dubu biyu da hamsin za a samu sababin masu fama da wannan cutar har miliyan daya a duk shekara a kasashe masu tasowa muddin ba a dauki matakin da ya dace ba.

‘’Abin dadi shine ita wannan cuta ta sankarar bakin mahaifa na daya daga cikin sankarar da za a iya yin wani abu a kai. Mun ga yadda a kasashe da suka ci gaba aka samo kanta ta hayar yin cikakken gwaji. Cikakken gwajin ya hada da ba wai kawai yin gwajin gano ta ba a a har da yinsa akai-akai da kuma kula da aikin sosai da kuma gano cutar da samar da magani,' ya kara da cewa.

A zahiri kusan duk cututtukan sankarar bakin mahaifa ana kamuwa da su ne ta kwayar halittar virus mai suna human papilloma. Kuma ana daukarta ne ta hanyar saduwa. A kasashe masu arziki mafi yawancin mata sukan samu wannan gwaji akai-akai wanda ake kira Pap smear wanda hukumar WHO ta ce na rage hadarin kamuwa da wannan cuta da kashi casa’in cikin dari. Amma wannan gwaji ana yinsa a kan dala arba’in wanda ya yi tsada ga matan kasashe masu tasowa. Wani kwararre kan gwajin sankarar bakin mahaifa na hukumar lafiya ta duniya, Rengaswamy Sankaranarayanan ya ce akwai hanya mai sauki ta yin gwajin sanakarar bakin mahaifa. Hanya ta farko ya ce it ace ta gwaji da ido ta diga digon sinadarin vinegar a kan bakin mahaifa a inda likita ko ma’aikacin lafiya zai duba ya ga ko sinadarin vinegar din ya koma fari wato yana nuna alamar sankara. Hukumar lafiya ta duniya ta ce a yankunan Karkarar India wannan gwaji da kuma bayar da magani duk ana yi a kasa da dala hudu.

Kuma irin wannan gwaji na iya kare mace daga kamuwa da sankarar mahaifa har tsawon shekaru goma. Hukumar ta kuma ce ana iya rage kamuwa da cutar sankarar bakin mahaifa da rabi ta hanyar yin gwaji da kuma bayar da magani kamar yadda ya kamata.

XS
SM
MD
LG