Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush ya tura babbar tawagar agaji yankin tekun India - 2004-12-31


Shugaba Bush na Amurka ya tura wata babbar tawaga zuwa Asiya dan nazarin irin taimakon da wadanda bala’in igiyar ruwan tsunamis ta shafa ke bukata. Sakataren harkokin waje, Colin Powell da dan uwan shugaban, Jeb Bush ne za su jagoranci tawagar.

Mai magana da yawun fadar gwamnati ta White House, Trent Duffy ya ce tawagar za ta tashi zuwa yankin a ranar lahadi. Ya kuma ce tawagar za ta gana da shugabannin yankin kan irin karin taimakon da Amurka za ta bayar. Ya kuma kara da cewa: ‘’ Tawagar na karkashin sakatare Colin Powell da gwamna Jeb Bush wanda ke da gogewa kan harkar aikin agaji a jihar Florida bayan da jihar ta gamu da wasu bala’oi daban-daba a baya.’’

Mista Duffy ya kuma ce Gwamna Jeb Bush zai nuna irin dagewar dangin Bush na taimakawa wadanda wannan bala’i na tsunamis ya shafa a yankin tekun India. Kakakin gwamnatin ya kuma ce shugaba Bush ya yanke shawarar tura wannan babbar tawaga ne saboda ya tabbatar da cewa gwamnati ta kula da bala’in kamar yadda ya kamata.

‘’Shugaban yana fatan tawagar za ta kawo masa rahotan irin yanayin da ake ciki don gwamnati ta bayar da taimakon da ya dace.’’Ya kara da cewa. Da aka tambayi kakakin gwamnatin ko wannan tawaga na nuna cewa Amurka na son bayar da taimakonta ne a ware sai ya ce a a Amurka na aikin agajin ne tare da sauran kasashen duniya da kuma majalisar dinkin duniya. Shugaba Bush ya ce alkawarin taimakon dala miliyan talatin da biyar da Amurka ta yi somin tabi ne kawai. Jami’an fadar gwamnati da na ma’aikatar harkokin waje na fama da kokarin kare korafe-korafen cewa taimakon da Amurka ke yi ya yi kadan.

A wani bayani ga ‘yan jaridu ranar Alhamis mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Richard Boucher ya yi watsi da zargin . ‘’Duk wani zargin cewa Amurka ba ta bayar da taimakon da ya kamata ba shi da tasiri kuma ba haka ba ne, kuma bai dace da abinda ya ke faruwa a yanzu ba kuma bai dace da abubuwan da suka faru a baya ba.’’ Har yanzu babu tsarin aikace-aikacen da tawagar za ta yi a yankin da ya ke a yanzu a ke tsare-tsaren. Amma da alama tawagar za ta yi kwanaki ne a yankin.

XS
SM
MD
LG