Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An harbe gwamnan Bagadaza harlahira - 2005-01-04


‘Yan sandan Iraqi sun ce ‘yan tawaye sun harbe gwamnan gundumar Bagadaza har lahira. ‘Yan sandan sun ce Ali al-Haidari da mai tsaron lafiyarsa an kashe su ne ranar talata a lokacin da suke tafiya a cikin mota a garin Hurriyah na kusa da birnin Bagadaza. A wani hari kuma na daban, wani dan kunan bakin wake a wata motar daukan kaya makare da nakiyoyi ya maka motar a wani ofishin ‘yan sanda a tsakiyar birnin Bagadaza abinda ya kashe akalla mutane goma ya kuma raunata wasu sama da hamsin.

‘Yan tawayen na kai hare-hare kan manyan jami’an gwamnatin Iraqi da ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro a lokacin da suka zafafa kai hare-hare don ganin sun kawo cikas ga zaben da aka shirya yi a ranar talatin ga wannan wata na Janairu. A jiya litinin, akalla an kashe mutane goma sha takwas yawanci ‘yan sanda da masu gadi a wasu hare-haren kwantan bauna da hare-haren bama-bamai cikin motoci da garuruwa na arewacin Bagadazan.

XS
SM
MD
LG