Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan ya ziyarci yankin Aceh na Indonesiya - 2005-01-07


Babban magatakardar majalisar dinkin duniya ya kai ziyara yankin Aceh na Indonesiya inda yawan wadanda suka mutu sakamkon bala’in girgizar kasa da kuma igiyar ruwa mai karfi ta tsunamim ya kai dubu dari. Babban magatakardar, Kofi Annan ya kewaya Banda Aceh a ranar Juma’a ya kuma kewaya ne a jirgin sama mai saukar ungulu don duba irin barnar da tsunami ta yi a yankin.

Mista Annan ya gayawa ‘yan jarida cewa ya kadu da irin barnar da bala’in ya haifar. ‘’Mun kewaya zuwa gabar teku daga yamma kuma ban taba ganin irin wannan barnar ba, kuma dole mutum ya yi mamakin inda mutanen wurin su ke a yanzu,’’ in ji Kofi Annan. Babban magatakardar ya kuma ce wadanda suka rayu ba wai suna bukatar taimakon kasa-da-kasa ba ne kawai don ci gaba da yin rayuwa kamar yadda ya kamata amma suna bukatar kulawa ta musamman saboda irin kuncin da suka yi fama da shi. A Aceh, da dama daga cikin wadanda suka rayu ba sa iya tafiya saboda kaduwa kuma sun kasa fahimtar abinda ya same su.

Mista Annan ya zarto Aceh ne daga Jakarta bayan da ya halarci taron kasa-da-kasa kan tsara shirin agaji ga kasashen da suka gamu da bala’in igiyar ruwa ta tsunami a yankin tekun Indiya. Mutane sama da dubu dari da hamsin ne suka halaka sakamakon wannan bala’in kuma kashi biyu cikin ukunsu a Aceh.

Babban magatakardar majalisar dinkin duniyan ya nemi kasashe masu bayar da agaji da su raba kusan dala bilyan hudun da suka yi alkawarin bayarwa taimako cikin sauri don hana kara asarar rayuka daga cututtuka. A yanzu ana samun isar kayayyakin taimako zuwa yankin Banda Aceh amma ma’aikatan agaji da wasu mazauna yankin na korafin rashin saurin kai kayan agaji daga bangaren majalisar dinkin duniya. Amma Mista Annan ya ce batun ba haka bane domin mambobin majalisar na bukatar lokaci wajen tsara shirin wannan baban agajin.

Ya ce, ‘’ ina ga babu adalci a ce mun gaza, muna iya kokarinmu. Kuma ya kamata a gane cewa ita kanta majalisar na da girma kamar yadda mambobinta suke. Amurka da Japan da Australiya da kuma Indiya su ne da farko ke jagorantar shirin aikin bayar da agajin amma yanzu shirin na karkashin majalisar dinkin duniya.

XS
SM
MD
LG