Jerusalem An bayar da bayanin cewa an kashe daya daga cikin maharan a musayar wuta. Mai magana da yawun Isra’ila ta tabbatar da kai harin a wani matsagunin yahudawa na Morag da ke kudancin zirin Gaza. Ta ce mayakan sun dasa wani bam ne a kusa da wata motar soja sannan suka bude wuta kan wadanda ke cikinta.
Kuniyar Palasdinawa ta Islamic Jihad ta dauki alhakin kai wannan harin amma daya daga cikin masu magana da yawun kungiyar ya ce sun kashe dukkanin wadanda ke cikin motar. Wannan hari na safiyar laraba ya zo a bayan da Palasdinawa suka zabi Mahmuod Abbas a matsayin sabon shugaban kasar Palasdin da gagarumin rinjaye. Mista Abbas dai ya yi kamfen na neman kawo karshen tashin hankali da kuma komawa tattaunawar samar da zaman lafiya da Isra’ila.
Sabon shugaban bai yi wani bayani kan wannan hari ba abinda ya nuna a fili irin kalubalen da ke gabansa a lokacin da ya ke kokarin inganta danganta tsakanin Isra’ila da mayakan sa kan Palasdinawa.