Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana shirin tura jami’an tsaron Palasdinu zuwa  kudanchi Gaza - 2005-01-25


Ana shirin tura jami’an tsaron Palasdin zuwa kudancin Zirin Gaza a wannan makon bayan da tuni su ka bazu zuwa arewacin yankin domin hana kai hare-hare kan ‘yan Isra’ila. Wannan mataki ya zo a lokacin da alamu ke nuna cewa Isra’ila da Palasdin na kokarin tabbatar da dakatar da bude wuta a kuma lokacin da jakadan Amurka a Gabas-ta-tsakiya, William Burns ya doshi yankin a kokarin dawo da shirin samar da zaman lafiya.

Babu dai wata sanarwa kan wannan batu kuma da alama ba za a samu sanarwar ba amma a zahiri akwai alamun cewa bangarorin biyu na kokarin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya na wani lokaci. Bayan kamar tattaunawar kimanin mako daya a Gaza sabon zababben shugaban hukumar mulkin Palasdinawa, Mahmoud Abbas ya samu tabbacin wasu kungiyoyin mayakan sa kai na dakatar da kai hare-hare kan Isra’ila. Su dai mayakan sa kan sun dage ne kan dakatar da hare-haren na wani lokaci da sharadin ita ma Isra’ila za ta dakatar da kai mamayar soja da kuma kame da kuma kokarin yin kisan gilla kan Palasdinawa. Ita dai Isra’ila ba ta yi wani alkawari ba sai dai ta ce dakarunta za su yi abinda ya kamata muddin a ka samu sauyin yanayi.

A yanzu dai akwai ingantuwar al’amura a loacin da dubannin ‘yan sandan Palasdinu da sauran jami’an tsaro ke sintiri a yankin arewacin zirin Gaza domin hana kai hare-hare kan matsugunan Yahudawa. Jami’an tsaron Isra’ila da na Palasdinawa na ci gaba da tsara tattaunawa. Mista Abbas ya ce an samu damar da jami’an tsaron Palasdin za su iya isa sababbin wurare. Mataimakin firaministan Isra’ila Ehud Olmert ya yi na’am da kokarin Mista Abbas amma ya ce tasirin kokarin shine mahimmi.’’Muna murna da cewa yana kokari. Muna so mu ga ya samu nasara. Idan bai samu nasara babu wani abu da Israila za ta yi masa. Amma idan bai yi nasara ba to bai zama shugaban Palasdinawa ba kuma kokarin ya zama ba shi da amfani,' ya kara da cewa. Isra’ila ta ce dole ne Mista Abbas ya dakatar da ta’addanci idan ana son dawo da tattauna shirin samar da zaman lafiya.

Jakadan Amurka a Gabas-ta-tsakiya William Burns na kan hanyarsa ta zuwa yankin don tattaunawa da jami’an Isra’ila da na Palasdinwa kan yadda za a dawo da tattauna batun samar da zaman lafiya karkashin shirin kasa-da–kasa na taswirar samar da zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG