Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar dattijan Amurka za ta amince da nadin Rice a matsayin sakatariyar waje - 2005-01-26


Ana sa ran majalisar dattijan Amurka za ta amince da nadin mai ba da shawara kan tsaron kasa Condoleeza Rice a matsayin sakatariyar harkokin waje a yau laraba duk da irin rashin goyon bayan ‘yan Demokrat. Majalisar ta shafe ranar talata ta na mahawara kan batun.

‘Yan Demokrat sun yi amfani da wannan mahawara wajen kushe manufofin Bush kan Iraqi. Sun kuma zargi Madam Rice da sauran jami’an gwamnatin da yaudarar Amurkawa kan dalilan kai wa Iraqi yaki a lokacin da jami’an su ka yi amfani da zargin mallakar makamai masu hadari. ‘’Babban abinda ya ke damu na game da wannan batu shine nuna daya daga cikin babbar gazawar dimukuradiyya . A lokacin da shugabanni karkashin mulkin dimukuradiyya suka yaudari mutane kan yaki da kuma mamamye wata kasa, ina ga abin ya kai wani hali,’’ in jin Senata Dick Durbin dan Demokrat daga Illinois.

Shi kuwa Senata Robert Byrd na West Virginia daya daga cikin ‘yan majalisar masu kyamar yakin ya ce goyon bayan Madam Rice zai nunawa duniya ne cewa kamar mun sake amincewa da shirin gwamnati ne na kai hari kan kasashe da kuma daukar mataki ba tare da amincewar duniya ba da kuma watsi da tsofaffin abokanmu.

Amma Senata George Allen na Virginia karkashin Republican ya ce irin rashin goyon bayan da ‘yan Demokrat su ke nunawa Madam Rice da kuma kushe gwamnatin Bush yana nuna wani abu ne ga kasashen waje. Ya kara da cewa, ‘’ a kokarin kushe ta ya kamata a yi hankali ka da a zubar da kimarta a idanun kasashen waje. Wannan zai zama abu mai hadari ga kasarmu, ya kamata mu nuna hadin kai a cikin lamarin da fadada ‘yanci Senata Allen ya ce Rice ta yadda an yi kuskure a kan yadda gwamnati ta tunkari lamarin Iraqi sai dai ta ce sakamakon yakin yanzu an ‘yan tar da ‘yan Iraqi miliyan ashirin da biyar daga kangin tursasawar gwamnatin Saddam Hussein. Ba dai dukkanin ‘yan Demokrat ne suka ki goyon bayan nadin Rice ba . Senata Dianne Feinstein na California na daya daga cikin masu goyon bayan nadin na ta. Ya ce, ‘’ na yi imanin cewa ta na da kima kuma a shirye na ke da in yi aiki da ita a matsayin sakatariyar harkokin waje.’’ Su dai ‘yan Republican sun gamsu cewa Rice ta cancanci wannan mukami.

Senata Chuck Hagel na Republican daga Nebraska ya ce a matsayinta na ta hannun daman shugaba Bush za ta zama mai tsage gaskiya a gareshi. Kuma za ta gayawa shugaban abu mai dadi da mara dadi. Har ila yau idan ba ta yarda da wani ra’ayin gwamnati ba za ta fada na yi imani za ta fada.’’

Duk da rashin goyon baya daga ‘yan Demokrat ana sa ran Rice za ta samu amincewar majalisar a yau laraba don ta maye Colin Powell a matsayin sakatariyar harkokin wajen Amurka. Da an yi shirin jefa kuri’ar amincewar ranar Alhamis bayan da aka rantsar da shugaba Bush don yin wa’adi na biyu amma sai ‘yan Demokrat suka nemi da a daga jefa kuri’ar don a ba su karin lokacin yin mahawara.

XS
SM
MD
LG