Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kantoman Hong Kong ya yi murabus - 2005-03-10


Kantoman Hong Kong Tung Chee-hwa ya tabbatar da murabus dinsa abinda aka yi mako guda ana jita-jita akai kuma wannan ya kawo karshen mulkin yankin na shekaru takwas da ya yi. Mista Tung ya kasance kantoman Hong Kong na farko tun lokacin da Birtaniya ta bar yankin a shekarar alif da dari tara da casa’in da bakwai.

Mista Tung Chee ya danganta murabis din kan rashin koshin lafiyarsa amma da dama daga cikin mazauna Hong Kong suna ga akwai matsawar kasar Sin. Bayanan kafofin watsa labarai a Hong Kong suna da ra’ayin cewa jami’an kasar Sin sun kosa da irin rashin goyon bayansa. A watan Disamba shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yiwa Mista Tung dan shekaru sittin da bakwai kashedi abainmar jama’a saboda rashin tabukawa abinda ya jawo jita-jitan cewa Sin da niyyar sauke shi. Mista Tung dai ya karyata jita-jitan cewa kasar Sin ce ta tilasta shi sauka da mukaminsa. Ya ce,’’ wannan batu ba haka bane domin gwamnatin tsakiya ta sha fada cewa ni da abokan aiki na muna aiki kamar yadda ya kamata a Hong Kong.’’

Shi dai Tung ya fito daga wani gidan attajirai na Shangai yana da kuma kyakkyawar dangataka da Sin amma yana da karancin gogayyar siyasa. A lokacin da kwarjininsa ya fara raguwa ana ganinsa a matsayin dan anshin shatan Beijing kuma wanda bashi da dangantaka da marasa karfi. Goyon bayansa ga sabuwar dokar tsaro ta Sin da kuma rashin goyon bayansa ga zaben kai tsaye ya jawo jerin zanga-zangar siyasa a Hong Kong a shekarun dubu biyu da uku da kuma da hudu.

Shi dai wannan tsibirin da a da ke karkashin Birtaniya ya dawo karkashin Sin a shekarar alif da dari tara da casa’in da bakwai amma an yi mata alkawarin cin gashin kan siyasa. Sai dai akwai korafin cewa Sin din ta mamaye harkokin siyasar yankin. Ana sa ran Mista Tung zai bar ofis a ranar Asabar kodayake bai dai fadi lokacin barin ba. Babban jami’im gwamnati Donald Tsang dan wani dan sanda kuma gogaggen ma’aikacin gwamnati ne zai rike shugabancin har lokacin da za a zabi wani shugaban a shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG