Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rumsfeld ya damu da batun sayan makaman Venezuela - 2005-03-24


Sakataren tsaron Amurka Donald Rumsfeld ya nuna damuwarsa kan batun sayan bindigogi dubu dari da Venezuela za ta yi daga kasar Rasha. Mista Rumsfeld wanda ke kan ziyarar kasashen Latin Amurka ya nuna wannan damuwa ne ranar Laraba bayan tattaunawa da wani babban jami’in kasar Brazil.

Sakataren tsaron ya gana da mataimakin shugaban kasar Brazil da kuma ministan tsaro Jose Alencar. Jami’an guda biyu sun tattauna kan al’amura da dama wadanda suka hada da batun hana fataucin miyagun kwayoyi a yankin da kuma shirin yaki da ta’addanci a kan iyakokin kasashen Brazil da Argentina da Paraguay. Bayan taron, Mista Rumsfeld ya gayawa ‘yan jarida cewa Amurka ta damu da shirin Venezuela na sayan bindigogi dubu dari da kuma jiragen saman helikwaftan soja guda goma daga kasar Rasha. ‘’ Ina mamakin mai zai faru da wadannan bindigogi kirar AK47 har guda dubu dari. Na kasa gane me Venezuela za ta yi da su,’’ ya ce.

``Gwamnatin Venezuela ta ce tana bukatar wadannan makamai ne don ta kare kanta daga barazanar kasashen waje. Amurka na fargabar cewa wannan shirin makamai na kimanin dala miliyan dari da ashirin ka iya jawo gasar mallakar makamai a yankin kuma ya jawo rashin jituwa a tsakanin Venezuela da makwabatanta. Kuma Amurka ta damu matukla don fargabar cewa makaman ka iya fadawa hannun kungiyar FARC ta Colombia wadda Amurka ta dauka a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda. Sakataren tsaron na Amurka ya bayyana tattaunawarsu da Mista Alencar da cewa ta samu nasara. Ya ce sun tattauna batun shugabancin Brazil a aikin kiyaye zaman lafiyar kasar Haiti a inda take da dakaru dubu da dari daya da kuma kokarinta na tattaro dakarun kiyaye zaman lafiya daga Argentina da Chile da sauran kasashen Latin Amurka. Sai dai Mista Rumsfeld bai yi magana kan ko rawar da Brazil ke takawa a Haiti zai bata damar samun wakilcin din-din a kwamitin sulhuin majalisar dinkin duniya ba.

Brazil da Japan da Jamus da Indiya da Najeriya da Misra da Afirka ta Kudu sune kasashen da ake ta fada suna neman wakilcin din-din a kwamitin sulhun idan an fadada shi.

XS
SM
MD
LG