Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahoton sayar da man Iraqi ya soki Kofi Annan  - 2005-03-29


Masu bincike kan cin hanci a batun sayar da man Iraqi don sama mata abinci na shirin fitar da rahoton da ya soki babban sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan. Rahoton ya soki babban sakataren kan gazawar shugabanci wanda ya hada da dansa da kuma wani babban dan kwangilar harkar sayar da man.

Mista Annan ya kasa gano matsalar shigar dansa Kojo Annan cikin harkar wani kamfanin kasar Switherland wanda ya samu kwangilar fitar da man Iraqi don sayo mata abinci. Wannan na cikin rahoton da hukumar bincike ta Volcker wadda Kofi Annan ya kafa don binciken cin hancin dala biliyan sittin da biyar za ta fitar yau Talata. Tuni wasu ‘yan jaridu sun buga labari kan rahoton a ‘yan kwanakinnan.

Jaridar Wall Street Journal wadda ta fara buga labarin ta ruwaito cewa mutanen da suka ga rahoton sun ce rahoton ya nuna cewa Kofi Annan ya rufe idonsa kan abinda ke faruwa saboda dangantakarsa da dansa wanda ya samu damar amfana da harkar. Shi dai Kojo Annan ya yi aiki da kamfanin Cotecna na kasar Switherland a karshen shekarun alif da dari tara da casa’in amma ya bar aiki da kamfanin a dai-dai lokacin da kamfanin ya samu kwangilar samar da abinci ta dala miliyan sittin a Iraqi. Masu bincike sun ce Kojo Annan ya karbi kimanin dala dubu dari hudu daga Cotecna tare da wani kudi da ya rinka karba a kowane wata har zuwa farkon shekarar bara bayan da kwangilar ta kare.

Dab da fitar da wannan rahoton mai magana da yawun majalisar dinkin duniya Fred Echard ya ce Kofi Annan yana cike da imani duk da cewa akwai alamar ‘yar matsala a cikin batun. Ya kuma ce,’’ wannan kwangila an bada ita bisa ka’idojin majalisar dinkin duniya kuma kasancewar dan Kofi Annan na aiki a kamfanin bashi da wani tasiri kan bayar da kwangilar. Wannan shine abinda bincikensa ya nuna kuma ya yi imani da shi.’’ Mista Echard ya kuma ce Mista Annan ya ji zafi a matsayinsa na aiki da kuma na uba kan irin yadda aka kwarzanta batun dansa da kamfanin Cotecna. Sai dai ya ce Mista Annan zai haye wannan guguwar don karashe watanni ashirin da daya da suka rage masa..Ya ce,’’Mista Annan ba shi da niyyar yin murabus. Yana fatan za a wanke shi daga duk wani zargi.’’ Wannan rahoton da za a fitar na yau shine na biyu cikin guda uku na hukumar bincike ta Volcker. An dai fitar da na farko a watan Fabarairu za a kuma fitar da uku a tsakiyar wannan shekarar. Rahoton farko ya samu shugaban shirin sayar da man Iraqi don saya mata abinci Ben Sevan da laifi da kuma nuna san kai a harkar bayar da kwangilar.

XS
SM
MD
LG