Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren tsaron Amurka Donald Rumsfeld ya bukaci sabbin shugabannin kasar Iraqi da su zabi gwannan mutane su - 2005-04-13


Sakataren tsaron Amurka Donald Rumsfeld ya bukaci sabbin shugabannin kasar Iraqi da su zabi gwannan mutane su ba su manyan mukamai sannan kuma su guji duk abun da zai kawo jinkiri wajen girka demokradiya.

A jiya talata Mr.Rumsfeld ya gana da shugaban kasar Iraqi Jalal Talabani da kuma PM Ibrahim al-Jaafari a birnin Baghadaza. Haka kuma ya ziyarci sojojin Amurka sannan ya je arewacin kasar Iraqi domin ya godema shugabannin Kurdawa saboda rawar da su ka taka wajen kudutar da kasar Iraqi.

‘Yan tawaye sun zafafa kai hare-hare a yayin ziyarar ta shi. A birnin Mosul wata motar da aka cika da bama-bamai ta halaka fararen hula biyar. Wata motar, ita ma ta bama-bamai ta kashe mutane biyar a Tal Afar da ke yammacin kasar. Sannan kuma a yayin wata dirar mikiyar da su ka yi a kusa da kan iyakar kasar Syria wato Sham, sojojin Amurka sun kashe dumbun mutanen da ake jin cewa ’yan tawaye ne.

Har ila yau kuma, gwamnatin kasar Iraqi ta ce ta cafke Fadhil Ibrahim Mahmud al-Mashdani tsohon jigon jam’iyyar Baath ta Saddam Hussein, an kama shi ne bisa zargin shirya hare-haren da ’yan tawaye ke kaiwa.

XS
SM
MD
LG