Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A jiya talata sakatariyar harakokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta buga wayar talho ga jami’an kasashen Larabawa - 2005-04-13


A jiya talata sakatariyar harakokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta buga wayar talho ga jami’an kasashen Larabawa da na Turai domin neman goyon bayan su game da janyewar Israila daga Gaza.

Haka kuma tattaunawar ta da shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas da ministan harakokin wajen kasar Jordan Hani Al-Mulki, ita ma ta fi maida hankali ne ga ganawar da shugaba Bush ya yi shekaranjiya litinin da PM Israila Ariel Sharon. Har wa yau ta yi magana da jami’an Russia da na Jamus.

Daya daga cikin batutuwan da Mr.Bush da Mr.Sharon su ka tattauna a kai shi ne shirin Israila na gina sabbin gidaje a babbar unguwar Maaleh Adumim ta Yahudawa ’yan kaka gida a yammacin kogin Jordan. Mr.Bush ya ce, yin hakan ya sakama shirin kasa da kasa na neman cimma zaman lafiya a yankin GTT. Amma har a jiya talata an ci gaba da gina gidajen. Palasdinawa na matuƙar adawa da gine-ginen da ake yi a kusa da birnin kudus.

A halin da ake ciki kuma, ‘yan Israila masu adawa da shirin janyewar daga Gaza, sun sa sarkoki sun garkame kofofin makarantu 167 a yankin Tel Aviv a jiya talata kafin ’yan sanda su bi, su bubbuɗe su.

XS
SM
MD
LG