Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

kungiyoyin kare hakkokin marasa gata a kasar Kenya sun ce ya kamata  shugabar wata kungiyar yaki da cin hancin kasar Jamus da ke Kenya - 2005-04-19


kungiyoyin kare hakkokin marasa gata a kasar Kenya sun ce ya kamata shugabar wata kungiyar yaki da cin hancin kasar Jamus da ke Kenya ta koma bisa mukamin ta bayan da a makon jiya aka tilasta ma ta yin murabus bisa wani zargi.Ranar Juma’ar da ta gabata Gladwell Otieno, darektar kungiyar Transparency International reshen kasar Kenya ta yi murabus.

Magoya bayan ta sun fada a jiya litinin cewa jami’an kwamitin zartaswar ƙungiyar da ke kasar Kenya ne su ka tilastama Ms.Otieno yin murabus saboda ta ki rokon gafarar wani ministan gwamnatin Kenyar da ta yima zargin satar dukiyar jama’a kusan dala miliyan 11.Ms.Otieno ta musanta cewa ta furta irin wadannan kalamai.

Magoya bayan Ms.Otieno sun ce, maida ta bisa muƙamin ta zai farfaɗo da yarda da juna tsakanin jama’a da kungiyar Transparency International, wadda su ka ce, ta yi fice wajen neman hana gwamnatoci yin ha’inci.

Haka kuma sun ce shugaban kwamitin zartaswar kungiyar ta TI a kasar Kenya Joe Wanjui shi ne a sahun gaban gangamin neman kawar da Ms.Otieno daga mukamin ta, saboda abokantakar siyasar kud da kud dake tsakanin shi da shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki.

XS
SM
MD
LG