Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An samu fashewar nakiya sau biyu kusa da ofishin jakadanci na Birtaniya a birnin New York


An samu fashewar nakiya sau biyu kusa da ofishin jakadanci na Birtaniya a birnin New York da suka yi barna sai dai babu wanda yaji rauni.

yan sanda na bincike masababin hatsarin da kwamishinan yan sanda na birnin new york Ray Kelly yace wasu na’urori ne suka yi bindiga.

Mr Kelly yace an ajiye na’urar ne a cikin wani kwalin fulawa kusa da gini mai hawa goma sha hudu.

Magajin garin birnin newyork Micheal Bloomberg yace ba a san dalilin aje wannan na’urar ba, a ginin da ke da shaguna da ofisoshi da kuma ofishin jakandancin Birtaniya.

Wannan na’urar tayi bindiga ne yayinda aka fara kada kuri’a a babban zaben birtaniya.

XS
SM
MD
LG