Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yini Na Hudu a Zimbabwe,Shugabannin Siyasa Suna Ci Gaba Da Shawarwarin Hana Shirin Daunin Iko Rugujewa


Shugabannin siyasar ƙasar Zimbabwe na ci gaba da tattaunawa a rana ta huɗu domin gano hanyar kauda abinda ke hana ruwa gudu a shirin kafa sabuwar Gwamnatin Ɗaunin Iko a Zimbabwe.

Tattaunawar jiya Alhamis ba’a kai ga samun daidaituwa ba a kan waɗanda zasu riƙe ayyukan kula da wasu manyan ma’aikataun Gwamnati.

Idan an tuna a makon jiya ne shugaba Mugabe don raɗin kansa ya bada sanarwar miƙa ma’aikatun kula da ayyukan soja, da ta ’yan sanda da harkokin wajen Zimbabwe ga ’yan jam’iyyrsa ta ZANU-PF, su kuma ’yan hamayya suka ce basu yarda ba.

XS
SM
MD
LG