Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Kawayenta Sun Sami Sabanin Ra’ayi Da Rasha A Kan Iran


Sakatariyar harkokin Wajen Amurka Codoleezza Rice, tace Amurka da sauran kasashen duniya sun amince su ci gaba da iza wa Iran wuta, kan shirinta na inganta makamashin uranium, ciki kuwa har da kara tsananta mata takunkumi.

Rice ta shaidawa manema labarai bayan wani taro da tayi da takwarorinta na kungiyar Kawance ta NATO, a birnin Brussels yau Juma’a, cewa dukkansu sun amince da bukatar karin takunkumi kan Iran, idan dai taci gaba da inganta makamashin uranium, matakin dake kara kusanta ta da yiwuwar kera makaman nukiliya.

Sakatariya Rice ta kuma gana da Ministan harkokin Wajen Rasha Sergi Lavrov, a bayan fagge, amma dai babu alamun tayi nasarar shawo kan Rasha ta goyi bayan karin takunkumin.

Lavrov ya gayawa manema lkabarai cewa ai kamata yayi a ci gaba da tattaunawa da Iran kan wannan shiri nata da ta riga ta musanta.

XS
SM
MD
LG