Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da NATO Suna Tattauna Matsalar Afghanistan


Shugaba Bush na Amurka ya gana da Sakatare Janar na Kungiyar Tsaro ta NATO Jaap De Hoop Schaffer, a gidan gonarsa na Birnin Texas, domin tattauna al’amura da yawa, cikinsu kuwa har da tashe tashen hankulan da ake fama dasu a Afghanistan.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Condoleezza Rice da Sakataren Tsaro Robert Gates suna tare da Shugaba bush a wajen tattaunawar, wacce aka bude da wani cin abincin dare a jiya Lahadi.

Mai magana da yawun Fadar White House, Tony Fratto, yace yadda yawan mutanen dake mutuwa a Afghanistan ke daukar ra’ayin jama’a, yana daya daga cikin abubuwan da za a tattauna.

Dakarun Kungiyar NATO tare da na Amurka sunce ‘yan Taliban suna garkuwa da farar hula a duk lokacin da ake arangama dasu, al’amarin da kan jawo mutuwar farar hula masu yawa.

A wani labarin kuma, wani dan kunan bakin wake a gabashin Afghanistan, ya kashe mutum goma, ya kuma raunata kusan 35, lokacin da ya tashi wani bom dake jikinsa a wata kasuwa dake kauyen Gardez, a lardin Paktia, a daidai lokacin da wani ayarin dakarun kungiyar NATO suke wucewa.

XS
SM
MD
LG