Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Fara Zawarcin Syria Da Iran Kan Zaman Lafiyar Gabas Ta Tsakiya


Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka ta ce Amurka na shirin haduwa da Iraki da makwabtan ta, cikinsu kuwa har da Iran (Parisa) da Syria (Sham), domin tattaunawa game da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Iraki.

Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka Condoleezza Rice ta ce ta na fata Farisa da Sham za su yi amfani da wannan dama su kyautata huldarsu da Iraki, sannan kuma su maida hankulansu wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Rice ta ce jami’an kasashen da ke makwabtaka da Iraki, da Amurka da kuma sauran wakilan Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, masu kujera ta din-din-din za su hadu a birnin Baghadaza, a tsakiyar watan nan na Maris.

Ta ce mai yiwuwa ne wani taron ministoci ya biyo baya tun ma daga makon farko a cikin watan Afrilu. Rice ta ce tashin hankalin Kasar Iraki ya shafi makwabtan ta.

Ta ce kuma akwai rawar da wadannan kasashe da ke makwabtaka da ita, da kuma kasa da kasa za su taka wajen taimakawa gwamnatin kasar Iraki ta habaka zaman lafiya da dumke barakar da ke tsakanin ’yan kasa.a

XS
SM
MD
LG