Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Habaka Fasahar Rage Dogaro Da Man Fetur


Shugaba Bush ya halarci, wajen wani aikin gwajin samar da makamashi, a jihar Delaware, dake arewa maso gabashin kasar.

A jawabinsa ga mahalartan, Mr Bush yace dogaro a kan man fetur na kasashen waje, yana barazana ga harkokin tsaron kasa.

Ya kuma ce zai nemi majalisa ta bayar da izinin kashe kudi dala miliyan dubu biyu da dari bakwai, domin ci gaba da binciken sabbin hanyoyin samar da makamashi.

Mr. Bush yace a yau ya sanya hannu kan wani kuduri da yake tabbatar da niyyar gwamnati na cimma burin samar da sabbin hanyoyin samar da makamashi, kamar yadda ya fada a jawabinsa na daren jiya.

Yace gwamnatin taraiya zata sayi motocin nan da basa amfani da man fetur, da zarar an fara sayar dasu, domin ta rage amfani da man fetur da ake yi a ma’aikatunta, da kashi 20 bisa 100.

XS
SM
MD
LG