Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa Na Bikin Ranar Godiya ta Thanksgiving


Amurka tana wannan hutu ne tun zamanin shugaba Abraham Lincoln wanda ya Kaddamar da bikin a shekara ta 1863 (kimanin shekaru 143 kenan yau). Shugaban Amurka Franklin D. Roosevelt ya sanya hannu kan dokar da ta kebe Alhamis ta hudu cikin watan Nuwamba ta kasance ranar mika godiya a cikin shekara ta 1942.

Bikin na Farko farko da aka sani shine wanda Amurkawa ‘yan asalin kasar Ingila da suka gujewa mulkin mallaka, suka yi bikin barka da girbe amfanin gona tare da Amurkawa na asali watau indiyawa a jihar Massachusetts dake arewa maso gabashin Amurka.

A birnin New York, za a yi bikin ne da wani pareti na musamman da wani kanti mai suna Macy’s ya dauki nauyin kaddamarwa, a wasu sassan kuma miliyoyin Amurkawa na ta yin balaguro ta jiragen sama, na ruwa da na kasa, da kuma motoci domin sada zumunci da ‘yan uwa da abokan arzuki. Yin kabakin talo talo yana cikin al’adar wannan hutu.

Ahalin yanzu kuma shugaba Bush ya yanke shawarar yin wannan biki tare da yin afuwa ga talo talo biyu. Wakilin Muryar Amurka a fadar white House Scott Stearns ya ruwaito cewa an yi dace ba a sani tsuntsayen Talatalon masu suna “Flyer” da “Fryer” da kwayar cutar murar tsuntsaye ta ‘Avian flu’ ba. Basu kuma yiwa bil’adama ko wata halittar Allah laifin komi ba. Matsalarsu kawai ita ce kasancewa talo-talo a jajibirin hutun godiya, lokacin da Amurkawa watanda da namansu.

Akasin sauran miliyoyin tsuntsaye ‘yan uwansu, wadanda basu taki sa’a ba, Flyer da Fryer sun tsallake rijiya da baya yayin da shugaba Bush ya bada sanarwar ‘yanta su. Yace “ina ‘yanta su da safiyar nan domin su ci gaba da rayuwarsu cikin walwala da tsaro yadda ya kamata.

Tsuntsayen da aka fi samu a yammcin jihar Missouri ta tsakiya, sun isa birnin California inda za a karramasu a bukin faretin ranar godiya na Thanksgiving da ake gudanarwa a filin wassanni na Disneyland. Wadannan tsuntsaye sune rukuni na 59 da shugaban kasa ke ‘yantawa a ranar godiya ta kasa, wani biki da Amurkawa maza da mata ke murnar gudanarwa a ko wacce shekara.

A bikin da aka gudanar a lambun “Rose Garden”, shugaba Bush yace hutun Thanksgiving, lokaci ne da dukkan Amurkawa ke nuna godiya domin albarkatun da Allah ya yi masu. Yace “A gwaggwarmayar da muka sha cikin shekarun da suke shude, Amurka ta bunkasa daga kananan matsugunai a farkon kafuwarta, zuwa wata hamshakiyar kasa da ta ci gaba, ta kuma kasance mafi karfi a duniya”.

Ya kara da cewa Amurkawa sun kasance masu godiya a kowanne lokaci, suna kuma nuna irin wannan godiyar bana ma. “Muna godiya domin kyakkyawar kasarmu. Muna godiya domin wadatar abincin da zai ciyar da mu da sauran mutanen duniya. Muna godiya domin muna da yanci. Muna godiya domin iyalanmu. Muna kuma godiya domin rai da muke da shi kansha’, inji Shigaba Bush. Mr Bush ya godewa sojojin amurka da suka sadaukar da rayukansu domin kare kasarsu.

Shugaban na Amurka da Uwargida Laura, zasu yi hutun ranar godiyar a dandalin hutawa na Camp David dake bayan birnin Washington DC. Zasu dawo fadar White House ranar Asabar kafin su tashi zuwa Estonia da Latvia inda shugaban kasar zai halarci taron kungiyar kawance ta NATO. Zai kuma wuce zuwa Jordan domin wata ganawa da Prime Ministan Iraqi Nouri al-Maliki.

XS
SM
MD
LG