Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cimma Yarjejeniyar Kafa Gwamnatin Hadin Gwiwa A Kenya


Tsohon Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan, ya bada sanarwar cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakanin shugabannin siyasar kasar kenya domin kawo karshen rikicin siyasar da ya janyo zubda jini a kasar.

Wata sanarwar da ya bayar dazu a birnin Nairobi, Kofi Annan, yace idan an jima zai kira taron manema labarai domin bayanin dalla-dallar yadda aka cimma yarjejeniyar da yadda zata yi aiki.

A yau din ne kuma ake sa ran shugaba Mwai Kibaki, da shugaban ’yan hamayya Raila Odinga zasu sanya hannu kan daftarin cimma yarjejeniyar.

XS
SM
MD
LG