Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gabatar Da Kuduri A Kan Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya A Dafur


A wannan sabon kuduri dai, an bukaci girke dakarun hadin guiwar Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tariyar Africa, dubu 26 domin kawo karshen tashe tashen hankila a yammacin Sudan.

Kudurin wanda ke karkashin sashe na bakwai na dokokin Majalisar Dinkin Duniya, ya baiwa dakarun damar yin amfani da karfi wajen kare kansu da farar hular yankin Darfur.

Amma kuma jakadan Sudan a Majalisar Dinkin Duniya, Abdulmahmud Abdulhalim, ya soki kudurin, wanda yace ya cika muni.

Jamiā€™an sudan dai sun dage cewa wannan kuduri ya keta haddi da diyaucuin kasarsu. Jakadan Amurka a Sudan, Andrew Natsios, yace bai kamata Sudan ta sami wata dama ta hawa kujerar naki ba, a kan wannan batu.

XS
SM
MD
LG