Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbi Wani Kwamanda A Zimbabwe


Kafofin yada labaraun Zimbabwe sunce an harbi wani kwamanda soja, kuma na hannun daman Shugaba Robert Mugabe. Kafofin yada labaran sunce yunkuri ne na kisan gilla.

Jaridar Herald ce tace an harbi Kwamandan mayakan Sama Perence Shiri a hannu, daidai lokacin da yake tuka motarsa zuwa gona ranar Asabar.

Ministan Harkokin Cikin Gida Kembo Mohadi ya gaya wa Herald cewa da alamu wannan harin, daya ne daga cikin jerin hare-hare da aka tsara, a kan jami’ai da ma’aikatun gwamnati.

A kwanakin baya ma Shugaba Mugabe ya zargi jam’iyyar adawa ta MDC ta kitsa hare-haren ta’addanci, a kokarin da suke yi na kawo karshen gwamnatin sa, wacce ke kan mulki tun da kasar ta sami mulkin kai.

XS
SM
MD
LG