Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Goma Sha Biyar Sun Halaka a Pakistan,Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake


Jami'an Pakistan sunce dan harin kunar bakin wake ya kashe akalla mutane 15 ya jikkata wasu da dama a yankin kabilu kusa da kan iyakar Pakistan da Afghanistan. Hukumomi suka ce dan kunar bakin waken ya kai hari ne kan taron Majalisar magabata a gundumar Orakazai,inda aka fi samun zaman lafiya cikin yankunan Pakistan bakwai na kabilu da ke da kwariya kwariyar cin gashin kai.

Harin shine na baya bayan nan a jerin hare hare da ake kaiwa cikin 'yan kwanakin nan.Jiya Alhamis,akalla mutane 10 ciki har da yaran makaranta ne aka kashe lokacin da Bam da aka tada shi daga nesa a yankin Dir, dake arewa maso yammaci. Haka kuma wani dan kunar bakin wake jiya Alhamis, ya kai hari kan ginin hukumar yaki da ta'addanci a fadar kasar,Islamabad,ya raunata akalla mutane bakwai.

XS
SM
MD
LG