Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Minista A Lebanon


An bindige Pierre Gemayel, Minista a Gwamnatin Kasar Lebanon kuma Jagoran al’ummar Kiristoci. Shaidun gani da ido sunce ‘yan bindigar sun kaiwa motar da marigayi Gamayel ke ciki karo, a bayan garin Beirut, suka kuma bude wa motar ruwan harsasai. Daga nan aka wuce da Ministan, dan shekaru talatin da hudu zuwa asibiti, a inda ya cika.

Gamayel shine dan siyasa na baya-bayannan mai adawa da Kasar Syria da aka kashe a Lebanon cikin shekaru biyu. Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar, ya zargi jami’an Syria da hannu a kashe-kashen, ciki har da kisan gillar da aka yiwa mairgayi Prime Ministan Lebanon Rafik Al-Hariri a shekarar da ta gabata, a Beirut.

Syria dai tayi alla-wadai da wannan kisa, a wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labaran kasar ya bayar daga babban birninta San’a.

Daga Birnin Washington, Mataimakin Sakataren Harkokin Waje Nicholas Burns ya soki wannan hari, wanda ya baiyana a matsayin wani aikin ta’addanci. Ya kara jaddada goyon bayan kasar Amurka ga Prime Ministan Lebanon Fuad Siniora.

A farkon watan jiya, ministoci shida masu goyonm bayan Syria suka aje aikinsu, domin su mara baya ga bukatar kungiyar Hizbullah na ikon hawa kujerar naki a majalisar kasar. Tuni dai Hizbullah ta nemi a kawo karshen gwamnatin Siniora.

Marigayi Gamayel, ya fito ne daga cikin haular ‘yan siyasa, cikinsu kuwa har da mahaifinsa Tsohon Shugaban Kasar ta Lebanon, Amin Gamayel, da kawunsa Bashir Gamayel, wanda shima aka kasheshi a shekarar 1982.

XS
SM
MD
LG