Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Sojan Ruwa A Najeriya


Jami’an Najeriya sunce an kashe Sojan ruwan kasar daya,san nan wasu da dama kuma sun jikkata ,sakamakon hari da ‘tsagerun Niger Delta suka kai kan wani jirgin ruwan mayakan ruwan kasar a yankin Niger Delta mai arzikin mai a daren nan.

Fitacciyar kungiyar dake ikirarin fafutukar nemawa yankin Niger Delta yenci,da aki fi sani da lakanin MEND,tace ita take da alhakin kai wannan harin na Laraba,kan jirgin ruwan mai suna NNS Obula.

Cikin sanarwa da ta bayar,tace harin na yau sun kaishi ne domin nunawa hukuma cewa kasancewar Sojojin a yankin ba zai hana Kungiyar ta kai hari ko samarda kariya kan cibiyoyin mai idan har MEND tayi kuduri niyyar kai hari ba.

Haka kuma kungiyar tace ita ce da alhakin satar ma’aikatan mai ‘yan kasashen ketare guda shida na baya bayan nan cikin jirign ruwan kamfanin hako mai na kasar Italiya,da bashi da nisa da gabar teku a kudancin Najeriya.

Jiya Talata ce aka saki mutanen.

XS
SM
MD
LG