Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kunna Fitilar Wasannin Olympics Na Bana A Birnin Olympia Dake Girka


Yau Litinin ce a birnin Olympia mai tarihi dake Girka, aka kunna fitilar wasannin Olympics na bana, da za’ayi a Beijing.

An tsananta matakan tsaro, duk da haka wasu ‘yan zanga zangar nuna goyon bayan Tibet su biyu, sun kutsa kai har suka katse jawabin shugaban kwamitin tsara wasannin na China Liu Qi. Masu zanga zangar sun shimfida tutar dake neman kasashen Duniya su kauracewa wasnnain Olympics da za’ayi a Beijing.

Da gabatowar wasannin,kungiyoyi dake gwagwarmaya sun zafafa zanga zangar kan rashin mutunta hakkin bil-adama da China take yi,da kuma yadda ta riki matsalarTibet.

Masu goyon bayan Tibet suna kira da a soke bangaren bikin kewayawa da fitilar Olympics din da zai ratsa cikin Tibet.

Bayan an kammala bikin na yau,Fitilar zata yi balaguro zuwa Sin,sannan ranar Talatin 31 ga watan nan,fitilar zata fara rangadin sauran kasashen Duniya.

XS
SM
MD
LG