Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Wani Fim Na Batanci Ga Musulmi


Prime Ministan Netherlands, Jan Peter Balkenende ya godewa al’ummar musulmin duniya, saboda sunki yarda a tunzura su, ta hanyar fitar da wani fim mai nuna kyama ga Alkur’ani mai tsarki.

Wani dan Majalisar Kasar Netherlands mai ra’ayin rikau, Geert Wilders ne ya saka wani fim dandalinsa na yanar gizo, wanda gidan Talbijin na Netherlands yaki ya nuna, wanda ke nuna kyama ga ayoyin alkur’ani mai tsarki.

Fim din da aka sanyawa sun ‘Fitna’, yana nuno wasu hare haren ta’addanci, ciki har da wanda aka kai a nan Amurka, ranar 11 ga watan Satumban shekara ta 2001, kuma ya alakanta su da wasu ayoyin Kur’ani.

Wilders yace daya daga cikin manufofinsa na fitar da wannan fim, shine imani da yake da shi, cewar yawan shigar musulmi Kasar Netherlands, da ma sauran kasashen Turai, yana barazana ga akidojin dimokradiyya a kasashen.

Saidai Prime Minista Jan Balkenende, yace fim din bashi da wata manufa, illa ta musgunawa wani yanki na mutane, ya kuma yi watsi da ra’ayin fim din na danganta addinin musulunci da tashin hankali.

XS
SM
MD
LG