Wasu Sojojin k'asar Guinea Bissau masu bore sun kashe shugaban
k'asar Joao Beranrdo Vieira, jim kad'an bayan da wata fashewar bam ta halaka
hafsan hafsoshin sojojin k'asar.
Sojoji masu biyayya ga hafsan hafsoshin
da aka kashe, Tagme Na Waie, sun farma fadar shugaban k'asa da talatainin dare,
sannan su ka harbe shugaba Vieira a lokacin da ya ke k'ok'arin guduwa.
A cikin wata sanarwar da aka gabatar ta kafofin yada labaran gwamnati, rundunar sojojin k'asar sun ce sun shawo kan
al'amuran k'asar ta yammacin Afirka, amma rundunar sojojin ta yi kashedin cewa
ba fa za ta yarda da abun da ta kira 'yan kwasar ganima da 'yan tayar zaune
tsaye ba.
Haka kuma, rundunar sojojin ta ce za ta
mutunta kundin tsarin mulki , ta kuma kare demokrad'iya. Kundin tsarin mulki ya yi
tanadin cewa shugaban majalisar dokoki Raimundo Perreira shi zai kama ragamar mulki
har ya zuwa lokacin da za'a shirya yin zab'e cikin kwanaki 60 wato nan da watanni
biyu.
Da safiyar nan ta litinin k'ura ta lafa a Bissau, babban birnin k'asar Guinea-Bissau bayan an kwan dare cikin amon fashe-fashe bama-bamai da b'arin wutar bindigogi.