Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zakulo Mutane Uku Da Rai Daga Rusassun Gine Gine A Haiti


Al’ummar kasar Haiti jiya lahadi sun cika rusassun mujami’un birnin Port-au-Prince domin addu’a Allah ya kawo masu saukin matsalolin da girgizar kasar ta haifar.Ma’aiktan agaji kuma na ci gaba da laluben rusassaun gine-ginen suga ko za’a sami wadanda suka tsira, tare da zakulo gawarwakin wadanda suka halaka.

Tawagar jami’an ma’aikatan agaji na musamman daga Amurka ta zakulo mutane uku daga rusassun gine-ginen da ransu daga wata kasuwar zamani(Supermarket) a birnin Port-au-Prince. Kazalika sun sami sa’ar zakulo wani baturen Denmark daga rusasshen ginin ofishin MDD a birnin na Port-au-Prince.

A halin da ake ciki, miliyoyin ‘yan kasar Haitin da girgizar kasar ta rutsa dasu naci gaba galabaita tare da neman tallafin kayan abinchi, da ruwan sha, da magunguna. Jami’an agajin kasa da kasa sun koka da matsalar sufuri saboda rashin babban filin jirgin saman da zai dauki manyan jiragen saman kayan da ake turawa zuwa Haiti.

XS
SM
MD
LG