Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Baza Jita Jitar Sojoji A Najeriya Suna Shirya Juyin Mulki


Babban Kwamandan rundunar sojin Nigeria ya bada umarnin takaita kaiwa da komowar hafsoshin soja a Nigeria, ganin yadda al’amura ke neman rinchabewa saboda har an fara yada jita-jitar soja na shirin yin juyin mulki, ganin yanzu kasar bata da shugaban kasa.

Lt.Janar Abdulrahman Dambazau, jiya litinin yake shaidawa taron manema labarai cewa an baiwa duk hafsoshin sojin Nigeria umarnin takaita kaiwa da komowarsu a kowane sako na Nigeria, idan har tafiyar ta zama dole to sai a nemi izni.

Da yake magana kan zargi da ake yiwa rundunar sojoji a Jos na kisan kare dangi,Janar Dambazau ya karyata zargin,yana mai cewa, su a Soja basu karkasa kanus,walau bisa akida,ko jinsi ba.

Waje daya kuma babban hafsan harkokin tsaron Nigeria Air Marshal Paul Dike ya fito fili ya gargadi jami’an soja da kada su kuskura su hannu a harkokin siyasar Nigeria. Watanni biyu ken an shugaba Umaru ‘yar na Nigeriake kwance yana jiyya a wani Asibitin kasar Saudi Arebiya.

XS
SM
MD
LG