Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Dakon Sakamakon Zabe a Ghana


Jam’iyyar hamayya a zaben raba gardamar da aka gudanar a Ghana jiya, tana kan gaba da karamin rinjaye a kan jam’iyya mai mulkin kasar, a kuri’un da aka riga aka kidaya.

Rahotanni a yau Litinin sun nuna cewa John Atta-Mills na Jam’iyyar hamayya ta NDP, yana kan gaba a kur’un, inda Nana Akufo-Addo na jam’iyya mai mulki ta NPP ke bin bayansa daf da daf.

Saidai dukkan jam’iyyun biyu sunce an m,usguna wa magoya bayan su a runfunan kada kuri’a.

Mataimakiyar sakatariya Harkokin Wajen Amurka Mai Kula da Harkokin Afirka, tace Amurka na kallon Ghana a matsayin wata tauraruwar Afirka, mai haska turbar dimokradiyya.

Ta bukaci dukkan jam’iyyun biyu da su gudanar da al’amuran su cikin mutunci.

Daya daga cikin masu bin diddigin yadda ake gudanar da zaben daga kasashen waje, wanda har ila yau shine Mataimakin Shugaban Cibiyar Bincike ta Carter, John Stremlau yace sun gamsu da yadda aka gudanar da zaben cikin adalci.

XS
SM
MD
LG