Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaben Wakilan Majalisar Dokokin Iran Jummaa


Yau A Farisa ko Iran, al’umar kasar suke zaben wakilan shiga Majalisa, ana kuma sa ran cewa masu ra’ayin mazan jiya zasu ci gaba da rike madafar mulki,bayan an hana masu ra’ayin kawo sauyi takarar zabe.

Masu kada kuri’a zasu jefawa mutane dubu hudu da dari biyar dake neman cike kujeru 290 dake Majalisar dokokin kasar.

Zaben anayinsa ne tsakanin sassa biyu masu ra’ayin rikau,guda tana kusa da babban mai’ raayin mazan jiya shugaba Mahmud Ahmadinejad,daya bangaren kuma sune ke neman Iran tayi kyautata dangantaka wajen mu’amala da kasashen yammacin Duniya musamman kan batun shirin Nukiliyar kasar da ya jwo takaddama.

Majalsiar magabata,kungiyar Malamai dake sa ido kan lamuran kasar, ta hana ‘yan takara dubu daya da dari bakwai tsayawa zabe,wadanda aka hanan sune mutane dake da ra’ayin kawo canji,kuma masu hamayya da shugaba Ahmadinejad. Majalisar tace mutane da aka hana su takara,basu nuna cikakken goyon baya ga tafarkin tsarin mulki na Musuluncin kasar ba.

XS
SM
MD
LG