Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaman Dar Dar A Sokoto Bayan Yan Banga Sun Kashe Mutum Daya Suka Kona Gida a Unguwar Tudunwada


Anfara zaman dar dar a Sokoto,bayan wani harin da ‘yan banga suka kai kan wani gida a unguwar Tudunwada,suka kona gidan,sakamkon harin, an kashe mutum daya. Wan nan harin ya sa an fara fargabar ko irin rikicin Jos ya kunno kai cikin jihar.

Amma a hira da manema labarai Kwamishinan ‘yansandan Jihar,Abubakar Mohammed,yace wan tashin hankali baya da nasaba da addini ko kabila,kuma sulusin mazauna birnin basu ma san anyi wan nan rikici ba.Shima dayake magana kan tashin hankalin,Gwamna Aliyu Magatakarda Wamako,yace ya ziyarci sassa daban daban na fadar jihar, domin karyata jitar jitar da ake yadawa kan barkewar rikci. Yace makiya Najeriya da sokoto ke baza irin wan jita jita.

Da yake amsa tambaya kan rikicin Jos,Gwamna Wamako,ya aza laifin kan gwamnati jihar,sarakuna,da shugabannin addini,saboda yace, ko basa fadawa juna gaskiya,ko kuma abinda yake fita bakunansa daban,abinda suke aikatawa daban. Domin yace ba Jos kadai ake da musulmi da kirista a Najeriya ba. Meyasa sai acan ake yawan rikicin addini da kabilanci?

XS
SM
MD
LG