Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyiwa Sojojin Najeriya Da Suke Aikin Kiyaye Zaman Lafiya A Darfur Fashi


Majalisar Dinkin Duniya tace anyiwa wata tawagar Sojojinta dana Tarrayyar Afirka dake sintri kwanton bauna, aka kuma yi musu fashi a yankin Darfur na Sudan.

Ofishin hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniyan a Darfur yace mutane sittin dauke manyan makamai sun tare masu sintirin kan wata hanya kusa da Geneina, a yammacin Yankin Darfur ranar Laraba data gabata. Rundunar tace mutanen sun sace bindigogi,albarusai,tarho da kuma kudi daga hanun sojojin daga Najeriya .Babu rahoton jikkata.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya yayi gargadin cewa harin ‘yan fashi da wasu miyagu, yana hana ayyukan kungiyoyin bada tallafi dake kokarin agazawa mutane da akayi kiyasin sun kai milyan biyu da rabi wadanda sukarasa muhallansu. Rundunar kiyaye zaman lafiya ta hadin gwiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka har yanzu bata kai karfin da ake so ba,sojoji dubu tara ne take dasu cikin yankin.

XS
SM
MD
LG