Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Yace Har Yau Shine Mataimakin Shugaban Najeriya


Mataimakin Shugaban Kasar najeriya, Alhaji Atiku Abubakar yayi wata hira ta Musamman da Shugaban Sashen hausa na Muryar Amurka Sunday Dare, da Aliyu Mustapha Sokoto, inda ya karyata labaran dake cewa ya ajiye mukaminsa, ya kuma kara tabbatarwa da ‘yan najeriya cewa bashi da niyyar sauka, kuma yana kan hanyarsa ta komawa gida, da zarar ya kare hutunsa.

A wata hirar da yayi mai tsawon awa guda, daga gidansa dake unguwar Potomac, a Jihar Maryland ta nan Amurka, Alhaji Atiku Abubakar yace a bisa ka’idojin tsarin mulkin Najeriya, babu mahalukin da ya isa ya kore shi daga aiki, sai Majalisar Taraiya kadai.

Yace ba wani boyayyen abu bane cewa gwamnati mai ci, bata mutunta doka, domin yawan umarnin kotu da ta sa kafa ta take ba zasu lissafu ba. Saidai yace abin godiya ga Allah shine, rayuwar wannan gwamnati ta kusa karewa.

Da yake bayani a kan abin da ya kawo sabani tsakaninsu da Shugaba Obasanjo, Mataimakin Shugaban Kasar yace babban laifinsa gurin Obasanjo shine na kin amincewa da ayi tazarce, da kuma yadda yayi ta yaki da yunkurin na kara tsawon wa’adin gwamnatinsa.

Ya kuma jawo hankalin ‘yan najeriya, cewar har yanzu fa Shugaba Obasanjo bashi da niyyar bari gadon mulki, saidai idan abin ya zama lallai, kuma yace ya tabbata Shugaba Obasanjo zai yi duk abin da zai iya domin yaga shirin nan na mika mulki bai yi nasara ba. Yace lallai ‘yan Najeriya su lura, kuma su kwan da shirin tsare akidar da suka zaba, musamman a lokacin zabe.

Ya kara tabbatar da cewa Obasanjo fa ba zai tafi ba, sai ‘yan najeriya sun dage. Dangane da Asusun Horaswa Kan Fasahar Albarkatun man Fetur, Alhaji Atiku Abubakar yace bashi da wani abin boyewa, kuma baya tsoron Hukumar Hukunta Masu cin hanci da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa, saboda ya san baiyi wani laifi ba, ya kuma ce rahotanni da ake ta bazawa a kan laifuffuka da ake cewa yayi, mutane ne irin su Ministan babban Birnin taraiya, Nasir El-Rufa’i ke kitsawa.

XS
SM
MD
LG