Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Kotun Zimbabwe Zata Yanke Hukunci Kan Karar Da Yan Hamayya Suka Shigar Suna Neman A Bayyana Sakamakon Zaben Shugaban Kasa


Lauyoyin ‘yan hamayya a Zimbabwe sunce babbar kotun kasar zata dakata har zuwa Talata kamin ta yanke humunci kan kokarin ‘yan hamayya na tilasta a saki sakamakon zaben shugaban kasa.

Da yake magana da manema labaru litinin,lauyan ‘yan hamayya Alec Muchadehama,yace kotun ta amince tana da hurumin sauraron karar,amma ta jinkirta yanke hukunci kan batun da kwana daya.Jam’iyyar masu hamayya ta MDC tana neman a saki sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi kwanaki tara da suka wuce.

XS
SM
MD
LG