Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Zaben Amurka: Aski Ya Zo Gaban Goshi


A daidai lokacinda wuri ke dada kurewa ga zaben shugaban kasar Amurka, ‘yan takaran biyu, Barack Obama na jam’iyyar democrats da John McCain na Republicans suna maida hankalinsu akan jihohi da ke da muhimmanci ga duk mai son lashe wannan zaben – kamar jihohin Ohio da Pennsylvania.

A jihar Pennsylvania mai yawan kuri’u har yanzu Obama ke sahun gaba wajen tagomashin jama’a amma banbancinsa da McCain yana raguwa, don haka McCain ya zare dantse yana neman cimma Obama din, musamman a wurin mutanen da har yanzu basu yanke shawaran wanda zasu jefa wa kuri’unsu ba.

Yayinda McCain ke a Opennsylvania, mataimakiyarsa Sarah Palin na can tana kyamfen a jihar ohio, inda can ma kusan McCain da Obama suke kat da kat. Ba wani dan takaran shugaban kasa na Republicans da ya taba lashe zaben shugaban kasa ba tareda yaci wannan jihar ta Ohio ba.

Shima Obama yana can jihar ta Ohio, yana ta bayyana a sassa daban-daban na jihar yana kyamfe, wanda ke nuna cewa shi ma bai dauki jihar da wasa ba.

XS
SM
MD
LG