Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Kashe Akalla Mutane Ashirin Da Takwas A Bagadaza


Rundunar ’yan Sandan ƙasar Iraqi ta bada rahoton tashin wani bom da aka boye cikin wata mota wanda ya ratsa ta cikin gungun taron jama’a farar hula a birnin Bagadaza yau da rana.

A dai dai lokacin ne kuma wani ɗan ƙunar baƙin wake a gefe guda ya tada bom a jikinsa a dai dai lokacin da ’yan sanda da wasu ke ƙoƙarin kaiwa mutanen farko da suka jikkata agaji.

Mutane aƙalla 28 ne suka halaka. Ba wanda yace shike da alhakin kai waɗannan hare-haren, sai dai ana zargin hannun ƙungiyar al-qaidar Iraqi.

XS
SM
MD
LG