Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bhutto Ta Ja Damarar Yaki


Tsohuwar Prime Ministar Pakistan, Benazir Bhutto, tace zata yi jagorancin wani gangami a birnin Rwalpindi ranar Juma’a, don nuna adawrsu da dokar ta bacin da Shugaba Pervez Musharraf ya ayyana.

Jami’an Gwamnati a Rawalpindi dai sun lashi takobin hana wannan gangami wannan gangami ya gudana, amma Jam’iyyar Mrs. Bhutto ta PPP, ko Jam’iyyar Jama’ar Pakistan, tayi suna wajen iya hada kan jama’a a duk lokacin da tayi kira.

Dubban lauyoyin kasar dai suna ta gudanar da zanga zanga ba kakkautawa, suna kuma ta faman arangama da ‘yan sanda, a kokarin da suke yi na bijirewa dokar ta bacin da Shugaba Musharraf ya ayyana, wacce suka ce ta saba wa tsarin mulkin kasar.

Har yanzu dai jam’iyyun adawa basu fara gudanar da zanga zanga ba tukuna, amma dai masu lura da al’amuran yau da kullum sunce a halin yanzu ‘yan siaysar kasar suna cikin rudani, kan martanin da ya kamata su mayar.

Ana ganin idan har PPP ta gudanar da gangaminta ranar Juma’a, to hakika sauran jam’iyyun adawa zasu bi sahu.

XS
SM
MD
LG