Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Tace A Saki ‘Yarta Da Tsagerun Niger Delta Suka Sace


Ma’aikatar Harkokin Wajen Birtaniya, ta nemi a gaggauta sakin wata yarinya ‘yar shekaru uku mutuniyar Birtaniya da tsagerun yankin Niger Delta suka sace, tare da kashedin kada a kuskura a bari wani abu ya same ta.

‘Yan sandan Najeriya sunce an sace yarinyar ne daga cikin wata mota, lokacin da motar ke bin wani titi mai cinkoson motoci. Wata mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Nageriya, Ireju Barasua, tace an dauke yarinyar ne a kan hanyarta ta zuwa makaranta.

'Yan sanda sunce I zuwa yanzu dai basu san ‘yan wacce kungiya ne suka sace yarinyar ba. Ita ce karamar yarinya ‘yar kasashen waje ta farko da aka taba sacewa a yankin Niger Delta, daga cikin kimanin 200 da aka sace tun da tsagerun nan suka fara sace sacen nan kamar da wasa a shekara ta 2006.

XS
SM
MD
LG