Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom A Gefen Hanya Ya kashe Fasinja Goma Sha Sida A Iraqi


Yan sandan Iraq sun ce a kalla fasinjojin wata motar safa goma sha shidda ne suka mutu sakamakon tashin wani bom da aka dana gefen hanya a kudancin kasar. Kakakin rundunar yace motar tana kan hanyarta ne zuwa Nasariyeh daga birnin Basra dake gabar teku. A kalla mutane 22 kuma suka jikkata. Babu wani karin bayani a kan hadarin.

A wata dabam kuma, rundunar sojin Amurka tace wani harin bom da aka kai jiya Litinin, ya kashe sojojin Amurka uku da tafintansu a lardin Diyala. Yayinda a wani labarin na dabam rundunar tace harin kunar bakin wake ya kashe sojojin Amurka biyar yayinda suke sintiri a kar a Bagadaza.

XS
SM
MD
LG