Mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney,yace Hamas tare da goyon bayan Syria da Iran na neman hana shawarwari tsakanin Falasdinu da Isra’ila samun nasara.
Da yake magana da manema labaru yau a birnin kudus,Cheney yace akwai shaida cewa Iran da Syria suna goyon bayan Hamas.Ya zargi kasashen biyu cewa suna kai gwauro su kai mari a cewarsa, wajen ganin sun wargaza shawarwarin wanzar da zaman lafiya da akeyi ahalin yanzu.
Cheney yayi magana ne bayan ya gana da shugaban Isra’ila Ehud Olmert a wata ganawar karin kumallon safe.
A halin yanzu Cheney yana Ankara babban birnin Turkiyya a zango na karshe a rangadin kwanaki tara da ya kai yankin.