Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Da McCain Sunyi Alkwari Zasu Yi Aiki Tare.


Shugaban Amurka mai jiran gado Barack Obama,da abokin hamayyarsa a zaben shugaban kasa,John McCain,sun yi alkawarin zasu yi aiki tare kan matsalar tattalin arziki,da wasu manyan matsaloli da Amurka take fuskanta.

A jiya litinin,Mr. Obama ya gana fuska da fuska da Mr. McCain,a karo na farko tun kada Senatan daga Jihar Arizona, a zaben shugaban kasa da aka yi ranar 4 ga watan Nuwamban nan.

A sanarwar hadin gwiwa da mutanen biyu suka bayar,sunce sun gudanar da tattaunawa mai armashi kan bukatar kaddamar da sauyi.Haka kuma sun ce akwai bukata daukan matakin bai daya domin rage yawan barnar da ake yi a Gwamnati da mummunar hamayya a Washington da nufin sake farfado da amincewar da ‘yan kasa sukayiwa Gwamnati,da sake dawo da bunkasa, da yelwa ga dumbin Amurkawa masu kuzarin aiki.

XS
SM
MD
LG