Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Congo Sun Fara Nuna Alamar Janyewa Daga Gabashin Jamhuriyar Congo,Yayinda 'Yan Tawaye Kuma Suke Ci Gaba Da Dannowa Kan Birnin Goma,Fadar Lardi.


Dakarun gwamnati sun fara nuna alamar janyewa daga gabashin jamhuriyar Congo, yayin da ’yan tawaye ke ci gaba da kai hare haren da suka fara ranar Lahadi.

Rahotanni daga birnin Rutshuru sun ce rundunar sojin tana ficewa daga birnin bayan fito mu gama da suka yi da ’yan tawayen jiya Litinin da suka kuma ci gaba yau. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambaci ta bakin kwamandan rundunar sojin a arewacin lardin Kivu, Col Delphin Kahimci cewa, lamarin yayi muni kuma shi da dakarunsa zasu fice daga lardin ba da daɗewa ba.

An bada rahoton ɓarkewar wani faɗan a kudancin ƙasar kusa da garin Kibumba dake kimanin kilomita 20 daga arewacin Goma babban birnin lardin. An hakikanta cewa yan tawayen ƙarƙashin jagorancin janar Laurent Nkunda, suna neman iko kan babban birnin yankin.

Hukumar kula da yan gudun hijira ta MƊD tace dubban mutanen da faɗan ya tilastawa ƙauracewa matsugunansu sun fara isa sansanin dake da tazarar kilomita goma a arewacin Goma.

XS
SM
MD
LG