Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Lebanon da Kungiyar Fatah Sun Koma Bakin Daga


Ana iya jiwo rugugin manyan bindigogin atilary da makamai masu sarrafa kansu daga nisan kilomitoci, a lokacin da yaki ya kaure a kewayen sansanin ‘yan gudun hijira na Nahr al-Bared, kusa da Tripoli.

Ana iya hango dunkulen hayaki yayi sama, ya mamaye sararin subhana, a lokacin da yakin yayi tsamari. Fada tsakanin sojojin kasar Lebanon da mayakan kungiyar Fatah-ul-Islam ya kaure tun daga safiyar Lahadi, kuma ya rika tsananta.

Rundunmar Sojin dai ta tura daruruwan karin dakaru da tankokin yaki, wadanta suka farwa sansanin da ruwan harsashin atilary. Rahotanni daga sansanin Nahar al-Bared sunce mazauna sansanin dai mafaka suka dauka kawai a gidajensu, suka kuma zubawa sarautar Allah ido, a yayin da fadan ke ci gaba.

Har yanzu ba a san farar hula nawa wannan fada ya rutsa dasu ba. An dai dan tsagaita wuta na wani takaitaccen lokaci, saboda motocin daukar majinyata su sami damar kwashe wadanda suka jikkata, amma nan da nan sai fadan ya sake barkewa.

Wani Farfesan Nazarin Al-amuran Siyasa a jami’ar Amurka dake birnin Beirut, Sami Baroudi yace tun wasu watanni da suka shude ake ta tsoron faruwar wannan al’amari, saboda yadda aka ga ‘yan gwagwarmaya na ta samun makamai, suna kuma kara shiga sansanin.

Dama dai a iya cewa muna sa ran wani abu makamancin wannan ya faru, amma dai ba kazami kamar wannan ba. Ina ganin hatta sojoji da jami’an leken asiri, sun sha mamakin yadda mutanen nan suke da tsari.

Saboda haka duk da cewa hukumomi sa iya cewa wannan aiki ne na ‘yan ta’adda, ina gani hakika dan hakin da aka raina ne yake tsone ido. Wannan shine fada mafi muni tun daga karshen yakin basasar Lebanon.

XS
SM
MD
LG