Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gayyaci Manyan Kasashe Masu Arzikin Masana'antu Taron Koli Kan Matsalar Kudi, Anan Washington, Watan Gobe.


Amurka ta gayyaci shugabannin kasashe masu arzikin masana'antu,da wasu kasashe masu tasowa su halarci taron koli a Washington ranar 15 ga watan Nuwamba,da nufin tinkarar matsalar kudi da ake fuskanta.

Jami'an Fadar White House sunce an kuma gayyaci shugaban Majalisar Dinkin Duniya, na Asusun bada Lamunin Kudi(IMF),da kuma Bankin Duniya. Kakakin Fadar White Dana Perino, tace shugabannin zasu tattauna kan matakan da aka dauka domin magance rikicin na yanzu da kuma matakan hana irin haka sake aukuwa nan gaba.

Kungiyar da ake kira G-20,sun hada har da kasashe kamar China,India,Rasha,da kuma Brazil.

Ahalin yanzu kuma farashin mai ya fadi zuwa dala 66 da centi 90 kan kowace gangar danyen mai, a hada hadar yau a kasuwar New York,bisa tsoron koma bayan tattalin arzikin Duniya zata tilasta a rage bukatar mai.

XS
SM
MD
LG