Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Yi Fashin Wani Jirgin Dakon Kaya A Yankin Niger Deltan Najeriya


Rahotanni daga Nigeria na cewa wasu ’yan bindiga sun sace jirgin ruwan ɗaukan kaya tare da ma’aikatansa baki ɗaya dab da ruwan tekun yankin Niger Delta da ake rikici a kudancin Nigeria.

Har yanzu ba wata ƙungiyar da tace ita keda alhakin satar jirgin ruwan ɗaukan kaya na MV Thou Galaxy jiya lahadi a dai dai lokacin da ya shiga zangon sauke kayan da ya ɗauko a tashar jirgin ruwan warri. Kayan da jirgin ruwan yake ƙoƙarin saukewa mallakar kamfanin mai na Chevron ne.

Ba’a tantance ko daga wace ma’aikatan hjirgin ruwan suka fito ba, amma anji mai magana da yawun rundunar sojin Nigeria Rabe Abubakar yana cewa ga dukkan alamu mayaƙan ƙungiyar ’yan tawayen dake ƙarƙashin jagorancin Tom Polo ne suka kai harin.

XS
SM
MD
LG